Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan sanda sun kama Auwalu Dan Daba a Kano

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama wani da ake zargi ɗan daba ne mai suna Auwalu Ali, wanda aka fi sani da Auwalu Dan Daba, a Dorayi Quarters da ke Kano.

Wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin wadda Jami’in Hulɗa da Jama’a na ‘Yan sandan, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 31 ga Janairu a Kano.

Mutumin mai shekaru 26 ya shiga hannu ne bayan samun sahihan bayanai a kansa.

A cewar rundunar, jami’anta da ke aiki a Dorayi ne suka yi kamen bayan samun bayanai da ke danganta wanda ake zargin da hada kai da kuma shirya kungiyoyin ‘yan daba da ke kai hari da kuma yi wa jama’a fashi.

Sanarwar ta kuma ambaci wani lamari daban a Sharada Quarters, inda jami’an ‘yan sanda suka amsa kiran gaggawa da ya shafi harin da ake zargin ‘yan fashi da makami suka kai.

Rundunar ta bukaci jama’a da su kasance cikin shiri kuma su kai rahoton ayyukan da ake zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta lambar wayarsu ta gaggawa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use