An sako mutanen da aka yi garkuwa da su daga garin Kurmin Wali dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna a ranar Alhamis.
Daya daga cikin jagororin yankin ne ya bayyana hakan a ganawar da ya yi da wakilin kafar Daily Trust, inda ya ce mutanen sun shaki iskar ’yanci ne da tsakiyar daren Alhamis.
Sannan ya kara da cewa, sun jiyo amon manyan motoci sun shiga jejin Maro da ke yankin da ake zargi an kai wadanda aka yi garkuwa dasu.
Ya kara da cewa har yanzu basu da tabbacin ko su wane ne suka fito da mutanen.
Sannan basu da tabbacin ko duka mutanen da akayi garkuwa dasu din aka kubutar, haka kuma basu san ko an biya kudin fansa ko kuma ba a biya ba zuwa yanzu.
Zuwa yanzu al’ummar yankin na Kurmin Wali na ci gaba da daura ayar tambaya kan salon yanda aka kubutar da mutanen.
Idan za’a iya tunawa dai anyi garkuwa da mutanen ne kimanin su 177 yayin da suke tsaka da gudanar da ibadarsu a majami’a a ranar 18 ga watan Janairun da ta gabata.