Kungiyar Gwamnonin Arewa a Najeriya ta yi Allah wadai da harin da wasu ‘yan ta’adda suka kaddamar a jihar Kwara da ke tsakiyar kasar inda suka kashe mutum a kalla 160.
A wata sanarwa da Kungiyar Gwamnonin Arewa ta fitar, tayi Allah wadai da kisan mutane a jihar Kwara.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya yayi tir tare da Allah Wadai da kisan mutane a jihohin arewa da suka hadar da Jihar Kwara, Benuwai da kuma Jihar Katsina yana mai cewa hakan ta da zaune-tsaye ne cikin al’umma.
Gwamnan na wannan Martani ne sa’o’i kadan bayan kisan mutane a garin Moro da wasu ‘yan ta’adda suka yi tare da kona dukiyoyinsu a jihar Kwara.
Kazalika Inuwa, ya jajanta wa iyalan mamatan tare da tabbatar musu cewa Kungiyar Gwamnonin za ta tabbatar an hukunta masu hannu cikin wannan lamari.
Sanarwar ta kara da jan hankalin Gwamnatin Tarayya da ta zuba jami’ai da za su yi bincike don bankado wadanda suka aikata wannan ta’asar.