Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Amurka ta nuna bacin ranta kan kisan mutane a Kwara

Amurka ta nuna bacin ranta kan kisan mutane a Kwara

Gwamnatin Amurka ta nuna bacin ranta kan kisan mutane a ƙauyukan Woro da kuma Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, tare da yaba wa kan irin matakan tsaron da Shugaba Tinubu Bola Ahmed ke dauka.

Rahotanni sun nuna cewa, kusan rabin garin na Woro ne wannan iftila’in ya shafa inda dubban mutane suka rasu tare da kona dukiyoyin al’umma.

Kazalika, Dagacin garin na Woro ya ce kashi 95 na wadanda abin ya shafa musulmai ne.

A wata sanarwa da ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar a yau juma’a an nuna cewa a kalla sama da mutum 160 ne suka rasu yayin da ake ci gaba da fargabar karuwar adadin mutane da suka rasu.

Sanarwar ta mika sakon jaje ga iyalan mamatan tare da tabbatar da goyon baya ga gwamnatin Tinubu don kawo karshen ta’addanci a Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use