Majalisar ƙoli kan harkokin shari’ar Musulunci a Najeriya ta sake jaddada kiranta na a tsige shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Joash Amupitan, tana mai cewa ba ta da yaƙinin zai iya gudanar da adalci a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
Majalisar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban skatarenta, Nafi’u Baba Ahmad ya sanya wa hannu, inda ta ce kiran nata ba shi da alaƙa da addini ko ƙabilanci, sai dai damuwa kan sahihanci da amincewar jama’a ga tsarin zaɓe.
Majalisar ta tattauna batutuwan da suke da jibi da shugaban hukumar zabe, la’akari da kiraye-kirayen wasu jama’a na tsige shi saboda tuhume-tuhumen da ake masa na yi wa Najeriya zagon kasa.
Majalisar ta kara da cewa ba ta dauki bangaranci ba ko bambancin addini a kan zaman da ta yi ba, sai don kiraye kirayen al’ummar kasa da shakku da suke nunawa kann shugaban na IEC Amupitan.
Idan za a iya tunawa, ana zargin Amupitan da rubuta korafi ga Amurka tare da zargin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya tun kafun ya zama shugaban INEC.