Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Man United ta ci gaba da ba da mamaki a gasar Premier

Man United Man United
Wannan nasara ta sa United ta ci wasa huɗu a jere (Hoto: Getty Images)

Manchester United ta ci gaba da farfaɗowa a gasar Premier bayan doke Tottenham da 2-0.

United ta ci wasa huɗu a jere kenan yanzu tun bayan da Michael Carrick ya karɓi ragamar jagoranci.

Bryan Mbeumo ne ya fara ci wa ƙungiyar ta Old Trafford kwallo a minti na 38, inda daga bisani daf kafin a tashi kyaftin Bruno Fernandes ya ci ta biyu wadda kuma ta ba su nasara.

Tottenham dai ta kare da ƴan wasa goma a fili bayan bai wa Romero jan kati.

Nasarar ta bai wa Man United damar ci gaba da zama a matsayi na huɗu a teburin Premier da maki 44.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use