Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta fada cewa a yayin da ‘yan Najeriya ke raina jagororinsu, a can kasashen ketare kuma ana girmamasu.
Oluremi ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook a daren Juma’a bayan fitowarta daga wani taro a Amurka.
Har ila yau, ta ce mutane da dama na ganin shugabanni a matsayin abin ƙyama ko abin tsana a cikin Najeriya, duk da cewa a ƙasashen waje ana yabo da girmamasu saboda rawar da suke takawa da gudunmawar da suke bayarwa.
A cewarta, wannan rashin daraja da ake nuna wa shugabanni a gida ya samo asali ne daga “ƙiyayya da labaran ɓatanci” da wasu ‘yan siyasa ke yadawa a matsayin dabarar siyasa.