Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta ce ta kama mutum 11 waɗanda take zargi da aikata baɗala a wani otel a yankin Badariya da ke cikin birnin Kebbi.
Kwamandan hukumar a jihar, Malam Suleiman Muhammed ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Asabar, inda ya ce waɗanda suka kaman sun haɗa da mata takwas da maza uku.
Ya ce an kama su ne ranar Juma’a da daddare lokacin da suka kai samame yankin.
“An kama waɗannan mutane ne bayan samunsu da laifin aikata baɗala a cikin wani otel a birnin Kebbi,” in ji Suleiman.
Ya kuma ce hukumar za ta mika su zuwa kotu da zarar an kammala bincike.