Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Gwamnatin Kogi ta rufe kasuwanni don yaƙi da matsalar tsaro

Kogi state Kogi state
Gwamnatin jihar ta ce za a buɗe kasuwannin da zarar an kammala aikin samar da tsaro (Kogi State Government)

Gwamnatin jihar Kogi ta bayar da umarnin rufe wasu kasuwanni da kuma tashoshin mota a wasu sassan jihar, don yaƙi da matsalar tsaro da kuma kakkaɓe ayyukan yanbindiga.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kingsley Fanwo ya fitar, ya ce an ɗauki matakin ne don taimakawa aikin kakkaɓe ɓata-gari da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro yake yi tare da sauran jami’an tsaro a jihar.

“Mun ɗauki matakin rufe kasuwannin ne don taƙaita zirga-zirgar kayayyaki da hana masu aikata laifuka da masu kwarmata musu bayanai damar samun kayan abinci da kuma sauran tallafi,” in ji sanarwar.

Rufe kasuwannin da kuma tashoshin mota na wucin gadi ya shafi al’ummomi da ke ƙananan hukumomi bakwai na faɗin jihar.

Gwamnatin jihar ta ce za a ɗage matakin da zarar an kammala aikin samar da tsaro da ake yi a sassan jihar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use