Kungiyar manoma, masu sarrafawa da kuma ’yan kasuwar tumatir ta Najeriya (TOMAPMAN) ta fada cewa a bana farashin tumatir da sauran kayan lambu ba zai karu ba kamar yadda aka saba gani a duk lokacin Ramadan.
Shugaban kungiyar a jihar Kaduna, Malam Rabiu Zuntu, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar lahadi a jihar Lagos.
Zuntu ya ce, ana sa ran farashin kayan lambu zai kara sauka a lokacin Ramadan sabanin shekarun baya, saboda yawaitar noma da kuma raguwar bukata.
Ya kara da cewa azumin Ramadan na bana, wanda zai fara a watan Fabrairu ya kuma kare a Maris, ya zo ne daidai lokacin kololuwar girbin tumatiri.
Har ila yau, Zuntu ya bayyana cewa a halin yanzu, kwandon tumatir mai nauyin kilo 50 na bai wuce tsakanin Naira 7,000 zuwa Naira 10,000 a kasuwannin Arewacin Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa ’yan Najeriya kar su yi fargaban karin farashi a lokacin Ramadan sakamakon yawan tumatir da kuma karancin bukatarsa.