Wasu ‘yan bindiga sun halaka mutum uku tare da sace wani fasto Reverend Nathaniel Asuwaye a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
‘Yan bindigan sun kai harin ne a gidan faston da misalin karfe 3:20 na daren ranar Juma’ar da ta gabata a gidansa dake Karku a Karamar hukumar Kauru dake Jihar Kaduna.
Faston shi ne babban malamin cocin Katolika da ke ungwar Karku a karamar hukumar.
Sai dai a cikin wata sanarwa da cocin ya fitar ta bakin Reverend Jacob Shanet ya ce, bata gari ne suka kaddamar da harin don haddasa rigima a yankin.
Ya kara da cewa, wadanda aka kashe mazauna yankin ne, da suka hada da Jacob Dan’azumi da Maitala da Alhaji Kusari.