Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Masu zanga-zanga na ci gaba da mamaye Majalisar Dokokin Najeriya

Daga cikin masu zanga-zangar akwai dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar LP a zaben 2023 Peter Obi (Hoto: Others) Daga cikin masu zanga-zangar akwai dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar LP a zaben 2023 Peter Obi (Hoto: Others)
Daga cikin masu zanga-zangar akwai dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar LP a zaben 2023 Peter Obi (Hoto: Others)

Kungiyoyin fararen hula da na matasa da kuma na masu rajin kishin dimokuradiyya sun taru a harabar Majalisar Dokokin Najeriya don neman a amince da gyaran dokar zaɓe da ake takaddama kanta nan take.

Daga cikin abin da masu zanga-zangar suka bukaci a yi musu bayani kansa shi ne tanadin aika sakamakon zaɓe ta hanyar intanet kafin babban zaɓen 2027.

Masu zanga-zangar sun ce gyaran ya zama dole don tabbatar da gaskiya da kuma dawo da aminci a tsarin zaɓen Najeriyar.

Daga cikin masu zanga zangar akwai mambobin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da sauransu.

Gangamin ya kasance cikin kwanciyar hankali zuwa yanzu, inda jami’an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda da sojoji da kuma jami’an tsaron farar hula na Najeriya suka tabbatar da doka da oda.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use