Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

‘Yan bindiga sun sace Limami da Ladani a Filato

Ƴanbindiga Ƴanbindiga
Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da matsalar ƴanbindiga ta addaba (Getty Images)

Wasu ‘yan bindiga sun sace Limami da Ladanin wani masallaci a garin Dogon Ruwa da ke karamar hukumar Wase ta Jihar Filato.

Maharan sun kuma kashe mutum daya da sace wasu mutane shida.

Garin Dogon Ruwa na daya daga cikin garuruwan da ‘yan bindiga suka addaba wajen kai hare-hare a baya bayan nan.

Mazauna yankin sun tabbatar wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun yi awon gaba da mutanen ne yayin da suke tsaka da aikin gawayi wanda suke sayarwa.

Shugaban matasan karamar hukumar ta Wase, Shapi’i Sambo ya ce harin ya jefa tsoro da shakku cikin zukatan mazauna yankin.

Ya kara da cewa, bayan harin, al‘umma sun so su kai dauki amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.

Sannan ya ce zuwa yanzu, an kai jami’an tsaro da zummar samar da zaman lafiya a yankin tare da kwantar wa al’ummar garin hankali.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use