Rundunar ’Yan sanda a jihar Adamawa ta kama wani matashi da ake zargi da hannu a sace mahaifinsa a garin Malabu na karamar hukumar Fufore ta jihar Adamawa.
An cafke matashin ne tare da wasu mutum biyu bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai garin a ranar Talata.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, Suleiman Yahaya Nguroje ya fitar, an kama matashin ne bayan sace Alhaji Ahmadu da ya kasance mahaifinsa a ranar 30 ga Janairun 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda, waɗanda ke aiki tare da ‘yan sa kai na kungiyar Miyetti Allah, sun kai samame a wata maɓoyar da ake zargin ta masu garkuwa da mutane ce a ƙauyen Jera a karamar hukumar Fufore.
Mutane uku da aka kama da zargin sace jama’a su ne Lawali Haruna, mai shekaru 45 da Yahaya Ibrahim, mai shekaru 25, da kuma Da’u Alhaji Ahmadu, mai shekaru 28, dukkansu mazauna garin Jera ne a karamar hukumar ta Fufore.
Rundunar ta ce ana ci gaba da kokarin ceto wanda aka yi garkuwa da shi da kuma kama sauran mambobin ƙungiyar masu garkuwa da mutane, yayin da ake ci gaba da tsare waɗanda ake zargin tare da ci gaba da bincike.