Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

INEC ta tsayar da ranar zaben shugaban kasa a Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Najeriya INEC, ta ayyana ranar 20 ga watan Fabrairu a matsayin ranar zaben shugaban kasa na 2027.

Shugaban hukumar Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya kara da cewa, su ma zabukan ‘yan majalisun tarayya za’a gudanar da su ne a ranar da za’a yi na shugaban kasa.

Sannan za’a gudanar da na zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi kuma a ranar 6 ga watan Maris din shekarar 2027.

Shugaban hukumar zaben ya ce, shirye shirye sun kammala wajen tunkarar babban zaben na shekarar 2027.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use