Wata kotun Tarayya a Abuja ta bai wa Hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya umarnin gabatar mata da wani malamin addinin Islama Malam Shehu Sani Abdulkadir Zaria kafin ranar 18 ga watan Fabrairun da muke ciki bisa zargin kitsa juyin Mulki ga gwamnatin shugaba Tinubu.
Da yake ba da umarnin kama Shehin malamin, mai shari’a Peter Lifu ya ce wajibi ne a hukunta duk wanda yayi yunkurin saba dokokin kasa.
In dan za a iya tunawa a ranar 11 ga watan Disambar 2025 aka kama wanda ake zargin tare da killace shi da kuma hana iyalansa ziyartar inda yake rufe.
Lamarin ya sa wasu lauyoyi sun aike da takardar neman a saki Abdulkadir Zaria bisa abin da suka kira rashin bin ka’ida.
An fara takaddama kan neman kama malamin ne tun bayan da aka ce an ga wasu kudade a asusunsa wadanda aka danganta da wani jami’in gwamnati da aka ce yana cikin mutane da suka kitsa yunkurin juyin mulki.
Ko da yake iyalansa sun bayyana cewa wani masoyinsa ne ya mishi kyauta.