Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Atiku ya bukaci INEC da ta sake duba jadawalin zaben 2027 saboda watan Ramadan

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa da ta sake duba ranar 20 ga Fabrairu, 2027 da aka sanar don babban zabe mai zuwa, yana mai cewa akwai damuwa kan yadda azumin Ramadan zai kasance a tsakanin Musulmai.

Idan ba’a manta ba dai INEC ta tsara babban zaben 2027 a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar 6 ga Maris, 2027.

A cikin wani rubutu da ta wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, Atiku ya ce ranar da aka tsara ta zo a daidai lokacin Ramadan (7 ga Fabrairu – 8 ga Maris, 2027), lokaci mai tsarki na azumi da ibada ga miliyoyin Musulmin Najeriya.

Atiku ya jaddada cewa zabe yana bukatar tsare-tsare masu kyau, yana mai gargadin cewa gudanar da zabe a lokacin Ramadan zai iya shafar fitowar masu kada kuri’a da kuma shiga cikin harkokin zabe gaba daya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use