Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Majalisar dattawa ta gyara dokar zabe don bai wa INEC damar sauya jadawalin zaben 2027

Hoton majalisar dattawa yayin zaman amincewa da bashin Tinubu Hoton majalisar dattawa yayin zaman amincewa da bashin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya samu amincewar Majalisar Dattawa kan bashin dala biliyan 6 domin ayyukan more rayuwa

Majalisar dattawa ta amince da gyaran sashe na 28(1) na Dokar zabe ta 2022  wanda ya bai wa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) damar sauya jadawalin gudanar da zabubbuka idan bukatar hakan ta taso.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce kan ranakun zaben shekarar 2027.

An samu korafe-korafe daga bangarori daban-daban cewa ranakun zaben 2027 na iya yin karo da watan azumin Ramadan. Wasu fitattun ‘yan siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban Kasa, Atiku Abubakar, sun bukaci INEC ta sake duba jadawalin domin kauce wa matsalolin da hakan ka iya haifarwa ga masu zabe.

A zaman majalisar na ranar talata, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele (dake wakiltar Ekiti ta tsakiya), ya gabatar da kudirin sake nazari da mayar da dokar kwamitin domin gyara. Shugaban Kwamitin Majalisar kan INEC da Harkokin Zabe, Sanata Simon Lalong ( dake wakiltar Filato ta kudu), ya mara masa baya.

Gyaran da aka yi a bangaren “sanarwar zabe” ya tanadi cewa INEC za ta rika fitar da sanarwar zabe a kalla kwanaki 300 kafin ranar da aka ware domin gudanar da zabe. A baya dai dokar ta bukaci a yi hakan kwanaki 360 kafin zabe, wanda yanzu aka rage domin bai wa hukumar damar sassauci wajen tsara ranaku.

Tun da farko, INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘Yan Majalisar Tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da na gwamnonin jihohi da ‘yan majalisun dokokin jihohi za su gudana a ranar 6 ga Maris, 2027, bisa tanadin tsohuwar dokar.

Haka kuma, an samu muhawara kan Sashe na 60(3) da ya shafi yadda ake aika sakamakon zabe. Sanata Enyinnaya Abaribe ( dake wakiltar Abiya ta Kudu) ya nemi a kada kuri’a kai tsaye kan batun, inda gyaran ya amince da amfani da hanyoyin aika sakamako ta lantarki da kuma ta rubuce.

A sakamakon kada kuri’ar, sanatoci 55 sun goyi bayan matsayar Majalisar Dattawa, yayin da sanatoci 15 suka nemi a rungumi sigar da Majalisar Wakilai ta gabatar, wadda ta tanadi aika sakamakon zabe kai tsaye ta hanyar lantarki ba tare da jinkiri ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use