Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ramadan: Bauchi ta rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati

Gwamnan Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa ADC - Punch Gwamnan Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa ADC - Punch
Gwamnan Bala Mohammed na shirin sauya sheka zuwa ADC - Punch

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da rage lokutan aiki na ma’aikatan gwamnati a fadin jihar don azumin Ramadan na wannan shekarar ta 2026.

Gwamnatin jihar ta sanar da amincewar ne cikin wata sanarwa mai kwanan wata 17 ga Fabrairun 2026 kuma Daraktan Ayyuka a Ofishin Shugaban Ma’aikata, Ismail Ibn L. Garam ne ya sanya hannu.

A cewar wannan sanarwar, an yanke shawarar ne don baiwa ma’aikatan gwamnati Musulmi damar kiyaye ka’idojin Ramadan yadda ya kamata.

An bayyana cewa daga Litinin zuwa Alhamis, ma’aikatan gwamnati za su rufe da karfe 3:00 na rana, yayin da karfe 1:00 na rana a ranar Juma’a bai canza ba.

Wannan sanarwar ta kuma bukaci ma’aikata da su yi amfani da lokacin Ramadan don yin addu’ar ci gaba da zaman lafiya a jihar Bauchi da kuma Najeriya

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use