Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Rundunar sojin Najeriya ta kwato jirage marasa matuka daga hannun ’yan ta’adda

Operation Hadin Kai aa Cafke masu Hadin Kai da ’yan Ta’adda Operation Hadin Kai aa Cafke masu Hadin Kai da ’yan Ta’adda
Operation Hadin Kai aa Cafke masu Hadin Kai da ’yan ta’adda

Dakarun rundunar sojojin Najeriya na hadin guiwa a arewa maso gabas, karkashin Operation Hadin Kai, sun kama wasu da ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda tare da kwato drones da kayan aiki a hare-hare da suka gudana a jihohin Adamawa da Borno.

A wata sanarwa da aka fitar a Maiduguri, Mai Ba da Bayanin Yada Labarai na Theatre Command, Lt. Col. Sani Uba, ya ce dakarun Sector 4 na 28 Task Force Brigade, tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai da mafarauta, sun kama wani matashi mai shekaru 28, Ismail Muhammed, a yankin Visik da ke Karamar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. An bayyana shi a matsayin mai kai wa ’yan ta’adda kayan aiki.

Hakazalika, a wani samame da aka kai a Karamar Hukumar Madagali, dakarun sun yi kwanton bauna a layin kogin Visik inda suka hallaka wani kwamandan ’yan ta’adda mai suna Abdullahi Mafa, tare da kwato bindiga kirar AK-47 da harsashi mai cike da alburusai.

Bugu da kari, bisa sahihan bayanan sirri, an kama wani dattijo mai shekaru 64, Dauda Gubula, a tashar mota ta Madagali, wanda ake zargi da taimaka wa ’yan ta’adda da kuma samar musu da drones.

An kwato daga hannunsa drones guda biyu, kayayyakin hadin su da kuma na’urorin adana wutar lantarki na hasken rana guda 20. Rundunar ta ce ana kai wa ’yan ta’adda drones din ne domin amfani da su wajen kai hare-hare.

A bangaren Sector 2 kuma, dakarun Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai da Civilian Joint Task Force (CJTF) sun dakile yunkurin ’yan ta’adda a Ngamdu, Jihar Borno, inda suka hallaka wani da ake zargi da leken asiri tare da kwato wasu kayayyakin aiki.

Rundunar ta jaddada kudirinta na ci gaba da murkushe duk wata barazana ga tsaro a yankin Arewa maso Gabas tare da hadin kan al’umma.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use