Wasu jam’iyyun siyasa uku sun ce ba su ga sunayen ƴan takararsu ba a zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a jihar Kano.
Jam’iyyun da lamarin ya shafa sun haɗa da PDP da NNPP da kuma jam’iyyar haɗaka ta ADC.
Sai dai, hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC ta ce a shirye take wajen gudanar da sahihin zaɓe a mazaɓun Municipal da Ungogo.
Kwamishina zaɓen Kano, Abdul Zango ya ce hukumar ta bai wa kowace jam’iyya dama.
Sai dai, cikin sunayen ƴan takara na ƙarshe da hukumar ta fitar sun nuna babu sunayen ƴantakarar jam’iyyun NNPP da PDP da kuma ADC.
Ana gudanar da zaɓen ne don maye gurbin kujerun ƴan majalisar jiha biyu waɗanda suka rasu a bara.