Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

An harbe wani mutum bayan kutsawa gidan Trump na Mar-a-Lago

Jami’an sirri na Amurka sun harbe tare da kashe wani matashi da ya yi yunƙurin kutsawa cikin shingen tsaro a harabar hutu na Shugaba Donald Trump da ke Mar-a-Lago a jihar Florida.

Jami’an sun ce mutumin, dan shekara 20, yana ɗauke ne da bindiga da kuma galan na mai. An harbe shi ne da misalin ƙarfe 1:30 na safiyar Lahadi, daidai da 06:30 agogon GMT.

A lokacin da lamarin ya faru, Trump yana birnin Washington DC, ba ya Mar-a-Lago. Hukumar ta ce babu wani mutum da ke ƙarƙashin kariyarta da ya kasance a wurin lokacin faruwar al’amarin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anthony Guglielmi, ya ce jami’ansu tare da wani mataimakin jami’in tsaro na gundumar Palm Beach sun tunkari mutumin ne bayan ya nufi daya daga cikin kofofin shiga Mar-a-Lago. An tabbatar da mutuwarsa bayan jami’an tsaro sun harbe shi.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin, ciki har da tarihin mutumin da ayyukansa da yiwuwar dalilinsa na kutsawa wajen.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use