Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Dimokuradiyya na fuskantar barazana a karkashin mulkin Tinubu-Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yace dimokuradiyya na cikin hadari

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa dimokuradiyya Nageriya na cikin mawuyacin hali a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Atiku ya nuna damuwarsa ne kan karancin masu kada kuri’a da aka samu a zaben kananan hukumomi na babban birnin tarayya, Abuja.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce karancin fitowar masu zabe alama ce mai nuna barazana ga makomar dimokuradiyya a karkashin gwamnati mai ci.

Ya ce duk da haka, ba su yi mamakin abin da ya faru a Abuja ba, duba da yadda gwamnati ke ci gaba da matsin lamba da kuma tauye wa ‘yan adawa hakkokinsu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya ya zargi gwamnatin Tinubu da jam’iyyar APC da daukar matakan da ke ci gaba da tauye ‘yancin dimokuradiyya, inda ya ce ana kallon ra’ayin ‘yan adawa a matsayin barazana maimakon wata dama ta ci gaban kasa.

A cewarsa, idan ‘yan kasa suka fara yanke kauna cewa kuri’unsu ba za su yi tasiri ba, hakan na nuni da cewa dimokuradiyya ta fara shiga hadari.

Atiku ya yi kira ga shugabanni da su tabbatar da samar da yanayi mai adalci da ‘yanci, domin karfafa gwiwar ‘yan kasa su ci gaba da ba da gudummawa ta hanyar kada kuri’a.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use