Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya sallami Kayode Egbetokun daga mukaminsa na sufeto janar na ‘yan sandan kasar.
Manyan jami’an ‘yan sanda da majiyoyi daga Hukumar Kula da aikin ‘yan sanda ne suka tabbatar da tsigewar.
Tinubu ya kuma nada Tunji Disu, wanda a baya ya kasance mataimakin sufeto janar mai kula da sashen binciken bayanan laifuka na rundunar ‘yan sanda (FCID) da ke Alagbon a Legas, a matsayin sabon sufeto janar.
Rahotanni sun bayyana cewa matakin cire Egbetokun ya samu amincewa tsakanin jami’an ‘yan sanda.
Wata majiya ta ce jami’ai sun nuna farin ciki lokacin da labarin ya bayyana a ranar Litinin.
Ana sa ran sabon Sufeto Janar, Tunji Disu, zai mayar da hankali wajen gyara martabar rundunar ‘yan sanda, tare da tabbatar da bin ka’idoji da dokokin aiki kamar yadda dokar kasar da ‘yan sanda ya shimfida .
Masu sharhi kan harkokin tsaro na ganin cewa wannan sauyi wata dama ce ta sake fasalin rundunar, musamman wajen magance zarge-zargen cin hanci, nuna son kai da kuma karfafa yaki da manyan laifuka a fadin kasa.