Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

DSS ta kama wanda ake zargi da kai hari cocin Owo

Jami’an Hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun kama mutum na shida da ake zargi da hannu a kai hari cocin St. Francis Catholic Church da ke Owo a shekarar 2022, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da masu ibada 40.

Mutumin mai suna Sani Yusuf, ya shafe kusan shekara huɗu yana ɓuya kafin a cafke shi a Iguosa, ƙaramar hukumar Ovia ta Arewa a jihar Edo.

Rahotanni sun ce Yusuf babban kwamanda ne a ƙungiyar ISWAP kuma ana zarginsa da hannu a harin Owo da wasu hare-hare da suka hada da farmaki kan sansanin soji a Suleja da kuma garkuwa da mutane a jihar Kaduna.

Kama shi na zuwa ne bayan da tuni DSS ta gurfanar da wasu mutum biyar kan zargin ta’addanci.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa wannan mataki babban ci gaba ne wajen tabbatar da adalci da kuma yaki da ta’addanci a Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use