Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Bishop-Bishop na Katolika sun yi gargadin yiwuwar samun karancin masu zabe a 2027

Ƙungiyar Bishop-Bishop na cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) ta yi gargadi kan raguwa sosai a yawan ‘yan ƙasa masu kada kuri’a tana mai cewa hakan na barazana ga dimokuradiyyar ƙasar.

A jawabi da suka fitar bayan zaman su na farko na shekara ta 2026 a Abuja, sun bukaci INEC, da Majalisar Dokoki, da hukumomin tsaro su dauki matakan dawo da amincewar jama’a ga tsarin zabe kafin zaben 2027.

Sakamakon bayanai na INEC ya nuna cewa halartar masu kada kuri’a ya sauka daga sama da kashi 60% a zaben 2003 zuwa kashi 23% kawai a zaben 2023.

Bishops sun kuma yi kira a tabbatar da gaskiya a cikin dokar zabe aka yi wa gyaran tare ta samar da ingantaccen tsaro, da karin wayar da kan jama’a.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use