Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar yara biyar sanadiyar gubar abinci
Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta fara kwato motocin Gwamnati daga tsofaffin kwamishinoni
Gwamnan Adamawa Fintiri ya sauya sheƙa zuwa APC

Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta fara kwato motocin Gwamnati daga tsofaffin kwamishinoni

Hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta fara kwato motocin gwamnati daga hannun wasu tsofaffin jami’ai da ake zargin sun ƙi mayar da su bayan kammala wa’adin aikinsu.

Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ya ce tun farko an aika musu da wasiƙun neman su mayar da motocin, amma wasu ba su bi umarnin ba, wanda ya sa aka ɗauki matakin kwato su domin kare dukiyar al’umma.

Daga cikin waɗanda aka kwato motocin a hannunsu akwai tsofaffin kwamishinoni da dama. Hukumar ta jaddada aniyarta ta ci gaba da kare kadarorin gwamnati da tabbatar da gaskiya da riƙon amana a jihar Kano.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use