Hukumar EFCC a ranar juma’ar nan ta sake gurfanar da tsohon ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami da matarsa Asabe Bashir da kuma ɗansa, Abdul’aziz a gaban kotu bisa wasu sabbin zarge-zargen almundahanar ƙudi.
An dai tisa keyarsu ne zuwa gaban alkalin kotun tarayya da ke Abuja, Justice Joyce Abdulmalik, biyo bayan wasu sabbin tuhume tuhume da ake masu.
Lauyan EFCC, Jibrin Okutepa SAN, ya shaida wa kotun cewa an sake gurfanar da waɗanda ake zargin ne bisa gyare gyare kan adadin kudaden da ake zargin su da karkatarwa, daga naira miliyan 325 zuwa naira biliyan 325, da kuma naira miliyan 120 zuwa naira biliyan 120.
Joeph Daudu SAN, wanda shi ne lauyan wadanda ake zargi bai nuna ƙin amincewa da sabbin sauye sauyen ba, hakan ya sa alkalin kotun bai wa lauyan EFCC damar ci gaba da bayani.
A ranar 12 ga watan fabrairun da muke ciki ne dai guda cikin alkalan kotun, Justice Obiora Egwatu ta janye daga sauraron shari’ar ta Malamin da iyalinsa.