Fadar shugaban ƙasar Najeriya, ta shawarci tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar da ya haƙura da siyasa ya koma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Wata sanarwa da mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ta ce dawowar gwamna Ahmadu Fintiri APC, ya nuna cewa Atiku ba shi da tasiri a jiharsa.
A cewar Onanuga, Fintiri ya ɗauke gaba ɗaya siyasar Atiku zuwa jam’iyyar shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Yayi ikirarin cewa, wannan abin da Fintiri ya yi ba ƙaramin nakasu zai kawo wa muradin Atiku Abubakar na zama shugaban Najeriya ba.
Rahotanni sun bayyana cewa a safiyar wannan juma’a ce, gwamnan jihar Adamawa, Fintiri ya sauya sheƙa zuwa APC tare da dukkanin mambobin majalisar zartarwas jihar dama duk wani mai fada aji a jam’iyyar PDP da ke jihar.
Sai dai bayanai na nuni da cewa, ɗan Atikun, wanda kwamishinan ayyuka ne a jihar ya ƙi bin gwamnan zuwa APC.