Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama wani mai suna Shafi’u Usman, wanda ake zargi da hannu a harin da aka kai Cocin ECWA dake Ayetoro, a Jihar Kogi.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kai harin ne lokacin da masu ibada ke tsaka da ibada a Cocin ranar 14 ga watan Disamba 2025. Hukumar tayi nasarar cafke Shafi’u Usman ne a maboyar sa dake jihar Gombe.
Yayin da yake amsa tambayoyi, Shafi’u Usman, ya amsa aikata laifin da ake tuhumarsa inda ya bada tabbacin da hannun sa a harin na cocin tare da amsa wasu zarge zarge na garkuwa da mutane a jihohin Niger, Kwara da Kogi.
Kazalika ya bayyana sunan wani Ibrahim Dattijo a matsayin wanda ke bashi gudummawa wajen ta’addanci a jihohin Niger, Kwara, Kogi dama Jihar Zamfara, kuma ya bayyana shi a matsayin mai sayar masa da makamai da harsasai.