Iran ta kai harin ramuwar gayya kan ƙadarorin Amurka a Gabas ta Tsakiya, ciki har da Bahrain, Kuwait, Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa, bayan harin hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila.
Rundunar juyin-juya- halin Iran ta ce dukkan cibiyoyin soja na Amurka da Isra’ila a yankin an kai musu hare-haren ban mamaki da makamai masu linzami, kuma za a ci gaba da hare-haren har sai an kakkaɓe abokan gaba.
A Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, an ba da rahoton mutuwar akalla mutum ɗaya da kuma daƙile wasu makamai masu linzami da Iran ta jefa.
A Bahrain an kai hari kan hedkwatar rundunar ruwa ta “5th Fleet”, ko da yake ƙasar ta bayyana harin a matsayin “ta’addanci da take mata hakki.”
A halin da ake ciki dai, ƙasashen Qatar, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa sun rufe sararin samaniyarsu, yayin da Qatar ta ce ta dakile hare-hare kafin su shiga ƙasar.
Yanzu haka yankin na Gabas ta Tsakiya na cikin fargaba, yayin da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka a Oman da Geneva ta tsaya bayan harin na Amurka da Isra’ila a kan Iran.
Tuni dai ƙasar Saudiyya ta yi Allah-wadai cikin “kakkausar harshe” da harin da Iran ta kai kan ƙasashen na gabas ta tsakiya, inda ta yi gargadin ɗaukar mummunan martani muddin Iran ta ci gaba da hakan.