Iran ta sanar da kafa majalisar riƙon kwarya mai mambobi uku domin gudanar da harkokin kasa bayan kisan Jagoran Addinin Kasar, Ayatollah Ali Khamenei.
An nada Ayatollah Alireza Arafi a matsayin daya daga cikin membobin majalisar wucin gadin. Sauran mambobi biyun su ne Shugaban Kasa, Masoud Pezeshkian, da Babban Alkalin Kotun Koli, Gholam-Hossein Mohseni-Ejei.
Malamin addinin mai shekaru 67, mamba ne a Majalisar Shura ta Iran.
Kamar yadda sashe na 111 na kundin tsarin mulkin Iran ya tanada, majalisar rikon kwaryar ce za ta jagoranci kasar har sai majalisar manyan malaman ƙasar mai mambobi 88 ta za bi sabon jagoran addinin, bayan kusan shekaru 37 na mulkin Khamenei.
Kisan da hadin gwiwar Amurka da Isra’ila suka yi wa jagoran addinin kasar, Ali Khamenei a ranar Asabar ya haifar da manyan tambayoyi kan makomar Iran a nan gaba.
Duk da cewa majalisar jagorancin za ta ci gaba da tafiyar da harkokin kasar a halin yanzu, kundin tsarin mulkin Iran ya bukaci majalisar malamai ta zabi sabon Jagoran addinin “da wuri-wuri.”