Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Matsalar tsaro ta raba sama da mutum 300,000 da muhallansu a jihar Neja

Gwamnan Jihar Neja da ke Najeriya, Umaru Mohammed Bago, ya bayyana cewa sama da mutum 300,000 ne suka rasa muhallansu a ƙananan hukumomi 10 na jihar sakamakon matsalar tsaro.

Bago ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan karɓar tallafin kayan jin ƙai daga gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin jin ƙai a Minna, babban birnin jihar.

Ya ce har yanzu ana ci gaba da kokarin tantance ainihin adadin mutanen da suka rasa matsugunansu, saboda hare-haren da ake ci gaba da kai wa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

“Zuwa yanzu, abin da za mu iya bayarwa kiyasi ne kawai. A taƙaice, muna da sama da mutane 300,000 da suka rasa muhallansu a fadin jihar Neja, a kananan hukumomi fiye da 10 da matsalar tsaro ta shafa,” in ji shi.

Gwamnan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin jihar na aiki tare da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da bai wa wadanda abin ya shafa damar komawa garuruwansu.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use