Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa, Joash Amupitan ya faɗa wa ‘yan Najeriya cewa hukumar ba za ta ba da tabbacin cewa komai zai tafi yadda ya kamata ba a zaɓen 2027.
Sai dai, ya ce hukumar na da ƙarfin aika sakamakon zaɓe ta na’ura a zaɓen 2027.
Amupitan ya yi jawabin ne ranar Lahadi a wani taron jin ra’ayin jama’a, inda ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su rage tsammani mai yawa, inda ya ce hukumar za ta yi ƙoƙarinta wajen gudanar da sahihin zaɓe amma ba za a iya cewa ba za a samu wata matsala ba.
Ya ƙara da cewa zaɓe ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya, kuma ilimantar da masu kaɗa ƙuri’a na da matuƙar muhimmanci.”
Shugaban INEC ya ƙara da cewa hukumar na da damar tura sakamakon zaɓe ta na’ura, amma babban ƙalubalen shi ne batun aikawa kai-tsaye a lokaci guda.