Hukumar kula da ayyukan shari’a ta Jihar Jigawa ta amince da tilasta wa wani alkalin kotun shari’a, Sadisu Muhammad Haruna, yin ritaya bisa zargin rashin da’a.
Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar, Abba Wangara, ya bayyana a Dutse cewa an ɗauki matakin ne bayan nazarin ƙorafi da shaidu da aka gabatar suka bayar.
Ya ce bincike ya tabbatar da laifin da ake zargin alƙalin na karɓar kuɗaɗen da ba su cikin jerin kuɗaɗen kotu da aka tanada a dokokin Shari’ar Jigawa na 2012, tare da kuma tsare wani ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan ƙorafin da Abdullahi Hamza ya shigar.