Gwamnatin Amurka ta gargadi ‘yan ƙasarta da ke zama a Najeriya da sauran ƙasashe da su yi kaffa-kaffa saboda karuwar tashin hankali tsakanin Washington da Tehran.
Wannan na dauke ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, inda ta yi kira ga ‘yan ƙasar su yi taka tsantsan musamman ma a wannan lokaci da kasar Amurkan da Isra’ila da Iran ke ci gaba da gwabza fada.
Sanarwar ta bayyana cewa hare-haren Amurkan da Isra’ila da kuma Iran ya shafi bangaren tafiye -tafiye da kuma kasuwanci a duniya.
Kazalika sanarwar ta shawarci ‘yan Amurka su yi rijista a shirin rijistar matafiya don samun sabbin bayanai na tsaro, tare da bibiyar shafuka da kasar Amurkan ta tanada don samun bayanai da suka kamata.