Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Babu hujjar da ta nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya, in ji Rasha

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya bayyana cewa har yanzu Moscow ba ta ga wata shaida da ke nuna cewa Iran na ƙirƙirar makaman nukiliya ba, yayin da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da kai musu hare-hare.

“Har yanzu ba mu ga wata shaidar cewa Iran na ƙirƙirar makaman nukiliya ba, wanda shi ne babba ko ma kawai dalilin yaki,” in ji Lavrov a Brunei.

Ya ce tuni aka fara jin tasirin hare-haren da ake kai wa Iran a fadin yankin, inda kasashen Larabawa suka fara fuskantar matsalar tattalin arziki da kuma asarar rayuka.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use