Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya gargaɗi ’yan jarida su yi taka-tsantsan da abin da ya kira ’yan siyasar ƙarshen zamani, yana mai cewa irin waɗannan mutane na iya lalata tsarin dimokuraɗiyya idan ba a kula ba.
Gwamnan ya yi wannan gargaɗi ne yayin wani taron buɗa azumin watan Ramadan da ya shirya tare da ’yan jarida a gidan Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna ranar Alhamis.
A jawabin da ya yi, Uba Sani ya ce wasu ’yan siyasa na amfani da bayanai marasa inganci ko kuma kalaman da ke iya tayar da rikici domin cimma manufofinsu na siyasa.
Majiyoyi daga wajen taron sun ce gwamnan ya buƙaci ’yan jarida su ci gaba da taka rawar gani wajen kare dimokuraɗiyya, yana mai cewa aikin jarida na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gaskiya da kuma kare haƙƙin jama’a.
Ya kuma jaddada cewa gudummawar ’yan jarida ta kasance ginshiƙi a tafiyar dimokuraɗiyya a Najeriya, tare da kira gare su da su kasance masu bin ƙa’idojin sana’arsu yayin da suke ruwaito al’amuran siyasa da na gwamnati.