Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, ya yi gargadin cewa rikicin da ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya na iya wuce gona da iri, tare da barazana ga tattalin arzikin duniya.
Faɗa tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran yana ci gaba da ƙara tsananta, lamarin da ya sa manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya ke kira cikin gaggawa da a dakatar da musanyan wutar tare da komawa tattaunawar diflomasiyya.
A wata sanarwa da aka wallafa a shafin Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Juma’a, Guterres ya ce hare-haren da ke faruwa a yankin sun riga sun haddasa mummunar illa ga fararen hula, kuma suna iya haifar da mummunan sakamako ga duniya baki ɗaya.
Ya ce duk wani hari da ya saɓa wa doka a Gabas ta Tsakiya da ma sauran wurare na janyo wa fararen hula tsananin wahala, tare da yin barazana ga tattalin arzikin duniya, musamman ga marasa galihu.
A wani bangare kuma, manyan jami’an agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi gargadin cewa rikicin na iya haifar da matsalolin jin ƙai da na tattalin arziki da za su wuce yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban hukumar agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar da ke New York cewa duniya na shiga wani lokaci mai matuƙar haɗari, yana mai cewa ana kashe kuɗaɗe masu yawa wajen yaƙi yayin da ake rage kasafin kuɗin tallafin agaji ga masu tsananin buƙata.