Wasu manyan malaman Shi’a masu ƙarfin faɗa aji a Iran sun yi kiran gaggauta zaɓar sabon Jagoran Addinin ƙasar bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya shugabanci ƙasar na tsawon shekara 36.
Wannan kiran ya zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar hare‑haren Amurka da Isra’ila.
Grand Ayatollah Naser Makarem Shirazi ya ce ya zama dole a zaɓi sabon jagora cikin sauri domin “taimaka wa tsara harkokin ƙasa yadda ya kamata.”
Haka kuma, Grand Ayatollah Hossein Nouri Hamedani ya yi kira ga Majalisar manyan malamai, wadda ke da alhakin zaɓar sabbin jagororin addinin da ta ƙara hanzarta aikin zaɓen domin daidaita shugabanci a wannan lokaci mai wahala.
A ƙarƙashin tsarin mulkin Iran, an kafa wata majalisar mulki na wucin gadi mai membobi uku domin su riƙe ikon jagoranci har sai an zaɓi sabon shugaban addini.
Kundin tsarin mulkin Iran ya ba Majalisar malamai damar ɗaukar har zuwa watanni uku kafin ta kammala zaɓen sabon Jagoran Addini, amma rikicin da ake ciki na iya zama kalubale kan yadda za a gudanar da zaɓen cikin lokaci.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya kamata ya kasance cikin masu zaɓen sabon jagoran addinin, ko da yake Tehran ta yi watsi da buƙatar hakan.