Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Hezbollah ta harba rokoki sansanin sojin Isra’ila

Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba jerin rokoki kan wani sansanin sojin Isra’ila a yau.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce mayakanta sun kai hari kan sansanin Ein Zeitim da ke arewacin Isra’ila da misalin ƙarfe 1:15 na rana agogon yankin (11:15 agogon GMT).

Hezbollah ta ce hare-haren na zuwa ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu birane da garuruwa a ƙasar Lebanon, ciki har da kudancin unguwannin birnin Beirut.

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a Lebanon ya kai 294, yayin da kamfanin dillancin labara na gwamnatin kasar ya ce mutum 1,023 ne suka jikkata tun daga Litinin 2 ga wannan watan.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use