Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Dakarun juyin juya halin Iran sun kai hari sansanin sojin Amurka a Bahrain

Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai wani harin makamai masu linzami kan sansanin sojojin Amurka da ke Juffair, Bahrain.

A wata sanarwa da IRGC ta fitar, ta ce harin ya biyo bayan wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa Amurka ta kai hari a wata cibiyar tace ruwa a tsibirin Qeshm, a mashigan Hormuz.

Rahotanni daga Bahrain sun bayyana cewa an ji ƙarar sautin na’urorin ankararwa (sirens) a wasu wurare, lamarin da ya sa ma’aikatar harkokin cikin gida shawartar mazauna yankunan da abin ya shafa su je amintattun wuraren ɓuya don kiyaye rayukansu.

Haka kuma, ma’aikatar cikin gidan Bahrain ta wallafa a shafinta na X cewa an samu tashin gobara da ƙonewar wasu gine-gine a Manama, babban birnin ƙasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use