Isra’ila ta kai hare-hare kan tankokin ajiyar mai a babban birnin Iran, Tehran, karo na farko tun bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan kasar, kamar yadda wani rahoton gidan talabijin na Isra’ila KAN ya tabbatar.
Kamfanin dillancin labaran Iran na gwamnati IRNA ya ce an kai harin ne kan wani wurin ajiyar mai da ke kudancin Tehran, yana mai bayyana cewa Amurka da Isra’ila ne suka kai harin.
Rahotanni sun ce wurin ajiyar man yana kusa da wani muhimmin matatar mai, sai dai kamfanin dillancin labarai na ILNA ya bayyana cewa harin sojin bai lalata kayan aikin matatar man ba.
A wani bangaren kuma, wani dan jarida na kamfanin AFP ya ruwaito cewa an ga wuta da hayaki na tashi daga wani wurin ajiyar mai da ke arewa maso yammacin Tehran bayan harin.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Iran, Isra’ila da kuma Amurka ke kara tsananta, inda bangarorin ke ci gaba da kai wa juna hare-hare.