Wani babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani ya ce an kama sojojin Amurka, ko da yake ya zargi Washington da ɓoye lamarin.
Larijani, ya bayyana a shafin X ranar Asabar cewa, “an sanar da ni cewa an kama wasu sojojin Amurka. Amma Amurkawa suna ikirarin cewa sun mutu ne a yaƙi.”
Ya ƙara da cewa “duk ƙoƙarin da suke yi na wofantar da batun, ba za su iya ɓoye gaskiya na tsawon lokaci ba.”