Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran ce ta kai hari kan wata makarantar yara ‘yan mata a garin Minab da ke kudancin ƙasar ta Iran.
Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a Amurka, Trump ya ce, bisa ga abin da ya gani, Iran ce ta kai harin saboda “ba su da daidaito ko saiti wajen amfani da makamai.”
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce har yanzu ana bincike kan lamarin, amma ya ƙara da cewa, Iran ce bangare ɗaya tilo da ke kai hare-hare kan fararen hula.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne a ranar 28 ga Fabrairu a makarantar Shajareh Tayyebeh a Minab, kuma hukumomin Iran sun ce fiye da mutum 150, yawancinsu ‘yan mata ƙanana ne suka rasu.