Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

China ta yi kiran gaggauta dakatar da hare-hare a rikicin Amurka, Isra’ila da Iran

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya yi kira da a dakatar da hare-haren soja nan take a Gabas ta Tsakiya, bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran da kuma martanin Tehran.

“Wannan yaƙi ne da bai kamata ya faru ba, kuma babu wanda zai amfana da shi”, in ji shi.

A wani jawabin da ya yi a wajen wani taro a Beijing, ministan ya ce “ƙarfi ba shi ne hanyar warware matsaloli ba; yin amfani da makamai zai haifar da ƙarin kiyayya ne kawai.

“Wang Yi ya nuna damuwar China game da rikicin da ke ƙara tsananta da kuma bukatar sasanci da tattaunawa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use