Majalisar malaman addini a Iran da ke da alhakin zaɓen sabon Jagoran Addinin ƙasar ta ce ta cimma matsaya kan wanda zai maye gurbin marigayi Ayatollah Ali Khamenei bayan kashe shi.
Ɗaya daga cikin mambobin majalisar, Ayatollah Mohammad‑Mahdi Mirbagheri ne yayi wannan bayanin.
Kamfanin dillancin labaran Iran na Mehr ya rawaito Mirbagheri yana cewa har yanzu akwai “wasu ƙalubale” da ya kamata a warware kafin a kammala dukkan matakan da suka shafi zaɓen sabon jagoran.
A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Iran, majalisar malaman addini mai mambobi 88 ce kaɗai ke da ikon zaɓen Jagoran Addinin ƙasar.
Khamenei, wanda ya jagoranci Iran na tsawon shekara 37, ya mutu ne bayan wani hari da Amurka da Isra’ila suka kai kan birnin Tehran a ranar 28 ga Fabrairu.