Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta buƙatar taimakon sojojin Burtaniya a rikicin da ƙasar ke yi da Iran.
A cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Truth, Trump ya ce ƙasarsa za ta iya cin nasara ba tare da amfani da jiragen dakon kaya guda biyu na Burtaniya da ake tunanin tura wa yankin ba.
Trump ya nunar da cewa Amurka ta yi mamakin yadda Burtaniya ta ɗauki lokaci kafin ta nuna goyon bayanta, inda ya ce ba sa buƙatar mutane su shigar musu yaƙi bayan sun riga sun yi nasara.
A baya dai furaiministan Burtaniya ya ƙi amincewa kasar Amurka ta yi amfani da sansanonin sojin kasarsa don kai wa Iran hare-hare.
Sai dai yanzu Burtaniya na tunanin tura manyan jiragen yaki zuwa Gabas ta Tsakiya, amma Trump ya ce ba ya bukatar taimako daga ƙasar.