Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Harin jirgi maras matuƙi ya lalata matatar ruwa a Bahrain

Gwamnatin Bahrain ta ce wani harin jirgin sama maras matuƙi da ake zargin Iran ta kai ya lalata wata matatar sarrafa ruwan teku zuwa ruwan sha, tare da jikkata mutum uku.

Ma’aikatar cikin gida ta Bahrain ta bayyana cewa harin ya faru ne da safiyar Lahadi, inda jirgin ya kai hari kan matatar ruwa wadda ake amfani da ita wajen samar wa al’umma ruwan sha daga ruwan teku.

Sai dai Iran ta mayar da martani da cewa Amurka ce ta fara kai irin wannan hari, tana mai zargin Amurkar da kai hari kan wata matatar ruwa a tsibirin Qeshm na ƙasar ta Iran.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce harin ya shafi samar da ruwa ga ƙauyuka kusan 30, kuma ya gargadi cewa kai hari kan muhimman ababen more rayuwa na iya haifar da mummunan sakamako.

A wani rahoto na daban, Bahrain ta ce ɓurɓushin wani makami mai linzami da Iran ta harba sun faɗi a arewacin ƙasar, lamarin da ya lalata wani ginin jami’a tare da jikkata mutum uku.

Kasashen yankin tekun fasha na da matatun ruwa kusan 400, waɗanda ke samar da kusan kashi 40 cikin 100 na ruwan sha da ake tacewa daga ruwan teku a duniya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use