Lokuta kadan bayan nada sabon shugaban addini an Iran Mojtaba Ali Khamene’i, Iran ta sake kai zafafan hare-hare kasar Isra’ila.
Rahotanni daga kafar yada labarai ta AFP ta ce Iran ta sake kai hare-hare sassan Isra’ila ta hanyar amfani da makamai masu linzami waɗanda a wannan karon ta yi ruwansu lokaci guda a yankunan kudanci da arewacin ƙasar.
Kafin yanzu Iran din na kai hare-hare ne daban-daban a sassan Isra’ila, sai dai ruwan makaman da Iran din ta yi a yau Litinin ya sha bambam, gabar da aka shiga mako na biyu da fara yaƙin ƙasashen.
Kazalika rahoton ya kara da cewa, an ji ƙarar na’urar ankararwa a birane da dama na Isra’ilar tun daga Haifa har zuwa Dimona.
Iran ta yi wa kasar Isra’ila gagarumar barna a hare-haren da ta ke kai wa, sai dai Isra’ila ta yi nasarar kakkabe wasu daga cikin makamai masu linzami da Iran din ta harba.
Rahotanni sun ce hare-haren sun shafi yankunan Tel Arad da Dimona waɗanda ke gaba da Negev, wato yankin da cibiyar binciken makaman nukiliya na ƙasar yake.
Haka-zalika an ji kuwwar ankararwa a Tiberias da tsaunukan Jezreel, Beisan da kuma kwarin Galilee.
Ko da yake Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa ta sanya kuwwar ne don ankarar da jama’arta, amma ba don hare-haren da Iran take mata suna tasiri ba.
Mazauna yankunan da Iran ta harba makaman dai sun ce sun ji ƙarar fashe-fashe, sai dai sun ce ba su da tabbacin ko ƙarar na’urorin da ke tare makamin da Iran ke aika wa ne ko kuma na saukar makaman ne.
A jiya ne dai kasar Iran ta amince da nadin Mojtaba Ali Khmanei, da ga marigayi Ali Khamenei wanda ya rasu a harin farko da Isra’ila ta kai a makon farko da fara yakin.